Wasu hare-haren jiragen sama da Amurka ta kai a kasar Libiya sun hallaka karin mayakan ISIS - wanda wannan ne karo na biyu da Amurka ta kai irin wadannan hare-haren a wannan kasa ta arewacin Afirka ciki kasa da mako guda.
"Tare da hadin gwiwar gwamnatin hadin kan kasar Libiya ta GNA, sojojin Amurka sun kai hare-haren jiragen sama da aka auna kan 'yan ISIS ranar Talata, inda mayakan ISIS din da dama su ka mutu," a cewar Rundunar Sojin Amurka mai kula da aiyukkan soji a Afirka, a wata takardar bayani da ta fitar.
Kwanaki hudu kafin nan, wasu hare-hare shida da jiragen sojin Amurka su ka kai, sun auna wani sansanin da ake amfani da shi wajen shigarwa da kuma fitar da mayakan ISIS a kasar, inda mayaka 17 su ka hallaka sannan uku daga cikin motocinsu su ka yi kaca-kaca.
Rundunar sojin Amurka din ta ce wannan sansanin, wanda ke a wuri mai nisan kilomita 240 kudu maso gabashin Sirte, ana kuma amfani da shi wajen shirya hare-hare da kuma boye makamai.