Amurka Ta Bukaci Bangarorin dake Yaki da Juna A Siriya Su Tsagaita Wuta

Ashton Carter, sakataren tsaron Amurka

A yau Litinin Amurka ta yi kira ga bangarorin dakarun Syria da na Turkiya da wasu sassan da ke da alaka da dakarun Kurdawa da Amurka ke marawa baya, da su dakatar da fadan da su ke yi a tsakaninsu, tana mai cewa ba za a lumunci hakan ba.

Wakilin Amurka na musamman da ke sa ido kan dakarun hadaka da ke yakar kungiyar IS, Bret McGurk, ya fada a shafin Twitter cewa, Amurka ba za ta amince da wannan arangama da ake yi a wannan yanki da babu ‘yan kungiyar ta IS ba, kuma al’amari ne da kasar ta Amurka ta ke cikin damuwa matuka akansa.

Yanzu haka an shiga yini na shida ke nan dakarun Turkiya tare da ‘yan tawayen Syria, na kokarin fatattakar dakarun Kurdawa da Amurka ke marawa baya daga garin Jarablus, da ke kan iyaka da Turkiyya.

Tare da samun goyon bayan Turkiyya, ‘Yan twayen Syria, sun samu su kwace ikon akalla kauyuka hudu da wani gari guda daga dakarun Kurdawa a yankin, a daidai lokacin da rahotanni ke ikrari da cewa, hare-haren sama da Turkiyya ke kaiwa sun yi sanadin mutuwar fararen hula 35.

Masu sa ido daga kungiyar Syrian Observatory for Human rights, mai bibiyan rikicin na Syria, sun ce wani hair da aka kai ranar Lahadiya halaka mutane 20 a kauyen Jub-al-Koussa, yayin da mutane 50 suka ji rauni a wani yanki da ke karkashin ikon wata hadakar mayaka.