Da yake mika takardan, jakadan Amurkan yace Amurka kanta ta zaku ta ga an kawo karshen ayyukan ta’addancin Boko Haram a yankin tafkin Chadi. Ya kuma kara da cewar samun wadannan jiragen yaki nan bada dadewa ba zai zama sanadin Boko Haram ta zama tarihi.
Babban hafsin hafsoshin rundunar saman Najeriya, Air Marshal Sadik Abubakar yace samun wadannan manyan jirage zasu baiwa mayakan saman kwarin gwiwa a yaki da ta’addancin Boko Haram. Yace jiragen suna da kayan zamanin da jiragen na yanzu basu dasu.
Air Marshal Ola Tocombo Ade Sanya, wanda shine darektan watsa labarai a helkwatan sojojin saman Najeriya, ya bayyana yanda za a yi hada hadar wadannan jirage. Yace kafin sanya hannu a kan wannan yarjejeniyar, rundunar sojojin saman Najeriya tare da takwarorinta na Amurka zasu yi nazarin yarjejeniyar kuma kafin karshen watan Faburarirun sabuwar shekarar 2018 zasu sanya hannu akai.
Your browser doesn’t support HTML5