Amurka Na Zargin Wasu Mutane Uku Da Yiwa Saudiya Aikin Leken Asiri

Twitter

Ma’aikatar harkokin shari’a ta Amurka ta tabbatar da laifin leke asiri a kan wasu tosfaffin ma’aikatan Twitter da suke leken asirin wasu masu amfani da Twitter a madadin gwamnatin kasar Saudi Arabia.

Wata kotun San Francisco ce ta tabbatar da laifin a kan Ali Alzabarah da Ahmad Abouammo da suka yi amfani matsayinsu suka zakulo bayanan wasu mutane da aka auna da suke amfani d Twitter.

Abouammo dai ba-Amurke ne kuma an kama shi ne a ranar Talata kana Alzabarah dan asalin Saudi Arabia kuma ya arce.

Mutum na uku, a cikin wannan batu shine Ahmed Almutairi dan asalin Saudiya, ana zarginsa ne da leken asiri da kuma shiga tsakanin bangarorin biyu, wato ma’aikatan Twitter da jami’an Saudiya.

Lauyoyi masu shigar da kara sun ce Abouammo ya shirya takardun boge kana ya yiwa jami’an hukumar binciken manyan laifuka a Amurka ta FBI karya.

An zargi Alzabarah da fitar da bayanan mutane sama da dubu shida da suke amfani da Twitter a cikin shekarar 2015, ciki har da bayanan wani dan asalin Saudiya kuma abokin Jamal Kashoggi, dan jaridar nan na Washington Post da ake zargin wasu mutane masu alaka da gwamnatin Saudi Arabia da kashe shi a cikin watan Oktoban shekarar 2018.