Amurka na tuhumar wasu mutane da suka ki jinin 'yan Somalia uku

Loretta Lynch sakatariyar shari'ar Amurka ko Antoni Janar

Masu gabatar da kara na Amurka sun sanar da tuhumar wasu mutane biyu bisa aikata laifukan tsana ko nuna kin jinin wasu mutanen Somalia guda 3 da suka farwa a birnin Dodge dake jihar Kansas a watan Yunin bara.

Ana tuhumar ta zargi mutane biyu da kai hari akan ‘yan Somalia din bisa dalilan wariyar jinsi da kuma bambancin kasar da suka fito.

Tare da zargin yin amfani da fasassun kwalabe wajen kai musu harin a ranar 19 ga watan Yunin da ya gabata.

Mutane kasar Somaliyar suna zaune ne anan Amurka a bisa ka’ida. Tuhumar da ake yiwa kowanne daga cikin masu laifin ta hada da daurin shekaru 10 a gidan yarin gwamnatin tarayya hade da tarar Dalar Amurka 250,000.

Saboda wannan laifin da ake tuhumarsu ya hada aikata laifin kin jinin wani wanda a karkarshin dokar gwamnatin tarayya ta Amurka laifi ne.

Jami’an tsaron farin kaya na FBI sun hada kai da ‘yan sandan birnin Dodge domin binciken lamarin.