Bukatar ta Washington ta kara tada hankali a kan yanda Amurka take sayarwa Isra’ila makamai da ake kashe dubun dubatan farar hula a yankin Falasdinawa tun lokacin da Hamas ta kai harin ta’addanci a kan Isra’ila watanni biyu da suka gabata.
Makaman da ake shirin sayarwa zasu kai dala miliyan 500 kana kwamitin huldar kasa da kasa da na harkokin kasashen ketare a mjalisar dattawa na tattance wannan bukata, kuma wannan bata cikin bukatar shugaba Joe Biden ta karin dala biliyan 110 da zai tallafawa kasashen Ukraine da Isra’ila.
Wani jami’in Amurka da bai so a bayyana sunansa ba, da kuma tsohon kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Josh Paul sun fadawa kamfanin dillancin labaran Reauters cewa ma’aikatar harkokin wajen tana matsawa kwamitotcin majalisar dokoki lamba da su sanya hannu a kan wannan hada hada cikin gaggawa, duk Allah wadai da kungiyoyin rajin kare hakikin bil Adama ke yi kan amfani da makaman da Amurka ke kerawa a wannan yaki.
Har ila yau, gwamnatin tana nazarin yiwuwar yin amfani da dokar fitar da makamai a matakin gaggawa don ba da damar fitar da wani adadi na harsashai da ya kai 13,000 a cikin 45,000, ba tare da izinin kwamitin majalisar ba, in ji jami'in na Amurka, koda yake ba a yanke shawarar karshe ba.