Yayin da dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ke kara tsami, Amurka na duba yiwuwar jibge wasu manyan makaman yakinta a Turai da Baltic don tauna tsakuwa
WASHINGTON, DC —
Amurka na duba yiwuwar girke manyan makaman soji a kasashe da dama na yankin Baltic da Turai, a cewar wasu jami'an gwamnati jiya Asabar.
An ce wannan shawarar ta nuna ma Shugaban Rasha Vladimir Putin cewa Amurka za ta kare kawayanta na kawancen NATO a gabashin Turai.
Jaridar New York Times ce ta fara bayyana wannan al'amarin a jiya Asabar.
Muddun aka amince da wannan shawarar, za a girke wasu daga cikin makaman ne a wasu kasashe da dama da ada ke karkashin tsaohuwar Tarayyar Soviet, a karo na farko tun bayan yakin cacar baka.