Amurka ta nuna goyon bayan ta ga hare-haren da Turkiya ta kai akan mayakan IS a Syria da kuma yankunan da ‘yan tawayen Kurdawa su ke a Iraqi.
A Jiya Lahadi, wani kakakin Fadar White House, ya ce hukumomin Ankara na da ikon su kai farmaki a yankunan ‘yan ta’adda, ciki har da wanda ta kai akan ‘yan jam’iyyar Kurdawa ta PKK a wani samamen dare da aka kai a ranar Juma’a arewacin Iraqi.
Harin da aka kai akan ‘yan jam’iyar ta PKK da aka haramta, shi ne na farko tun bayan shirin zaman lafiya da aka sanar a shekarar 2013.
Wadannan kalamai na Kakain Fadar ta White, na zuwa ne mako guda bayan barkewar wani rikici da aka dora alhaki akan kungiyoyin biyu, wadanda su kansu abokanan gaba ne.
Yanzu haraka Turkiya ta kira wani zaman na musamman a gobe Talata a tsakanin kasashen kawance na NATO domin tattaunawa kan matsalar tsaro da ta ke fuskanta.
Jam’iyar ta PKK ana ta banagren ta ce duk wani shirin zaman lafiya da aka cimma da Ankara ya ruguje bayan hare-haren sama da aka kai musu