Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce idan Rasha ta yi katsalandan a zaben Shugaban kasar Ukraine da za a gudanar ran 25 ga watan Mayu, Amurka za ta kakaba karin takunkumi wanda, a cewarsa, zai zabtare babban kaso daga tattalin arzikin Rasha.
WASHINGTON, DC —
A ganawarsu da Shugabar Sashen Hulda da Kasashen da ba su Tarayyar Turai Catherin Ashton a jiya Talata, Kerry ya ce Amurka ba fa za ta zuba ido kawai ba yayin da Rasha ke izi wutar tashin hankali. Ya ce ya zuwa yanzu ma takunkumin da aka kakaba sun fara yin illar gaske ga tattalin arzikin Rasha mai tangal-tangal, Kuma wai yanzu ma Amurka da kawayenta su ka fara.
Ashton ta bayyana zaben Shugaban kasar Ukraine da za a gudanar ran 25 ga watan mayu din da cewa mai matukar muhimmanci ne ga kokarin kawo kwanciyar hankali. Ta ce mutanen Ukraine ne za su yanke shawara kan ko mecece Ukraine da kuma abin da za ta kasance a gaba.
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya fadi jiya Talata cewa akwai waswasi game da sahihancin zaben saboda matakan soji da gwamnatin Ukraine ta dauka a gabashin kasar kan 'yan aware magoya bayan Rasha.