Amurka Na Duba Yiwuwar Cire Sudan Daga Jerin Kasashe Masu Taimakawa Ta'addanci

Amurka za ta yanke shawarar cire Khartoum daga cikin jerin kasashen da ke tallafawa ta'addanci.

A jiya Litinin, Amurka ta ce za ta sa ido sosai kan kudurin gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan ga mutunta 'yancin bil adama da dimokiradiyya da kuma zaman lafiya kafin Amurkar ta yanke shawarar cire Khartoum daga cikin jerin kasashen da ke tallafawa ta'addanci.

"Idan har duk bangarorin suna yin cikakken aiki, za mu hanzarta cikin sauri," in ji wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

An rantsar da sabon Firayim Minista a Sudan, Abdalla Hamdok, sanannen masanin tattalin arziki, wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya ta Sudan. Nadin nasa na zuwa ne watanni hudu bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, wanda ya kwashe kusan shekaru 30 yana mulkin.