Ma'aikatar Tsaron Amurka ta bayyana harba makamani mai linzamin da Koriya Ta Arewa ta cilla na bayan-bayan nan, a matsayin "wata babbar barazana" sannan ta ce ta na daukar mataki game da makami mai linzami na wannan kasa mai ra'ayin gurguzu.
WASHINGTON, DC —
Koriya Ta Arewa ta cilla makamai masu linzami guda hudu jiya Litini, wadanda uku daga cikinsu su ka yi tafiyar kilomita 1,000 har su ka fada cikin ruwayen Japan.
Wani mai magana da yawun hedikwatar tsaro ta Pentagon, Navy Captain Jeff Davis, ya gaya ma manema labarai cewa makaman masu matsakaitan zango ne kuma ba su wata barazana ga arewacin Amurka.
Davis ya ce harba wadannan makaman ya zo daidai lokacin atisayen shekara-shekara tsakanin Amurka da Koriya Ta Kudu kuma hakan ya yi daidai da dadadden tarihin takalar da aka san Koriya Ta Arewa da shi a daidai lokacin da mu ke atisayen soji da kawayenmu."