Amurka: Majalisar Wakilai Zata Kada Kuri'a Kan 'Yan Gudun Hijra daga Syria

 Paul Ryan, kakakin majalisar wakilan Amurka

Paul Ryan, kakakin majalisar wakilan Amurka

Yau Alhamis ne Majalisar wakilai ta Amurka zata kada kuri'a kan kuduri da 'yan Republican masu rinjaye suka gabatar, da nufin takawa shirin gwamnatin Obama birki na bada mafaka ga 'yan gudun hijira daga Syria da Iraqi anan Amurka. Shugaba Obama yana barazanar zai hau kujerar naki kan kudurin.

Jiya Laraba, sabon kakakin majalisar wakilan Amurka Paul Ryan yayi magana a zauren majalisar dangane da harin da 'yan ta'adda suka kai a birnin Paris ranar Jumma'a data gabata. "Dukkanmu mun kadu da abunda ya faru, amma duniya baki daya zata hada karfi, domin ganin ta'addanci bai sami galaba ba."

Kakaki Ryan yace hare haren tuni ne cewa, da akwai mugaye cikin al'umma, kuma ba za'a kauda kai ko ace an dabai baye su ba. Tilas a ga bayanta.

Yace Amurkawa sun damu tun bayanda aka kai hari a Faransa, saboda haka suke neman tabbaci cewa Amurka tana daukan dukkan matakai d a suka wajaba na tantance masu neman mafaka daga tarzomar da ake yi a Syria da kuma Iraqi.

Tuni dai kudurin yake fuskantar adawa daga wakilai 'yan jam'iyyar Democrat, har aka ji shugabansu Nancy Pelosi ta fito tana bayyana matukar adawa da kudurin na 'Yan Republican.