Rundunar sojin ruwan Amurka zata aika da kungiya domin neman jirgin saman daukar kaya da ya fado ya bace a kudancin tekun Pacific a watan Nuwamba.
Rundunar sojojin ruwan a cikin wata sanarwa da ta bayar tace “an san inda jirgin yake a kan ruwa kafin ya nutse, amma kuma zurfin teku a wannan wurin ya wuce tsawon kafa dubu 16, wanda yake yafi karfin kayyayakin kawo daukin da suke da shi”
An samu ceto mutane 8 kimanin mintuna arba’in bayan hadarin jirgin amman matukan jirgin guda uku sun bata a cikin teku, rundunar sojojin ruwan tace zasuyi iya bakin kokarinsu ganin sun nemo matukan jirgin da suka bace.
Kwararrun yan agajin da aka dauko daga birnin Washington zasu samu jagorancin shugaban binciken hukumar. Zasu kuma hau jirgin ruwa ne daga kasar Japan daga nan su zarce inda hadarin ya auku.