Amurka: Hukumomi sun kawar da 'yan tsagera da suka kwace wani gandun daji

Wasu cikin wadanda suka mamaye gandun dajin gwamnatin tarayyar Amurka

Kusan wata daya da aka kwashe ana kiki-kaka a wani dajin da ake aiye namun daji da ke arewa maso yammacin jihar Oregon na Amurka, tsakanin hukumomi da kuma ‘yan kungiyar wasu mutane masu makamai ta fara natsawa.

Hukumar binciken FBI da rundunar ‘yan sandan jihar ta Oregon sun ce an kama wasu mutane biyu ‘yan kungiyar, Duane Leo Ehmer da Dylan Wade Anderson a yammacin jiya laraba lokacin da suke barin dajin, da ake kira Malheur National Wildlife refuge. Mutum na uku mai suna Jason Patrick, shi kuma an kama shi ‘yan sa’o’I bayan kamen wadancan. Hukumomi sun fadi cewa sun gana da ‘yan kungiyar da rana, kuma kowannensu ya yarda ya mika kansa.

Wannan kamen ya zo ne kwana daya bayan da aka kama shugaban kungiyar, Ammon Bundy, da mabiyansa su 7 a wani shingen bincike da ke kan wata babbar hanya a lokacin da su ke kan hanyar zuwa wajen wani taro. An kuma kashe wani dan kungiyar mai suna Arizona Rancher Robert Finicum, yayinda ‘yan kungiyar suka yi musayar wuta da jami’an tsaro.

Hukumomi sun ce za a gurfanar da duk wadanda aka kama da laifin hana jami’an tsaro gudanar da ayyukansu ta yin amfani da karfi da kuma barazana