Jiya Alhamis kasashe goma da kasashen tarayyar Turai da kungiyar kasashen Afirka suka bada wa'adi inda suka suna sa ran madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar zai tattara nashi i nashi ya koma Juba babban birnin kasar tsakanin jiya da gobe Afirilu 23.
Kungiyoyin kasashen sun yi masa kashedi cewa idan ya yi kunnen shegu da wa'adin da suka bashi zasu gabatar da maganar gaban Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaro na kungiyar kasashen Afirka. Ba zasu tsaya nan ba. Zasu bukaci a dauki mataki.
Yakamata Riek Machar a ce ya koma Juba wannan makon domin a sake rantsar dashi mataimakin shugaban kasa da zummar kafa gwamnatin wucin gadi. Sai dai bai tafi Juba ba ranar Litinin da kuma Talata saboda rashin cimma jituwa akan adadin sojojinsa da zasu mara masa baya da makaman da zai iya shiga dasu birnin.
Ana ganin komawar Machar zata yi tasiri kan cigaba da shirin zaman lafiya da bangarorin biyu suka rabtawa hannu watan Agustan bara domin kawo karshen rikicin kasar da yanzu ya shiga shekaru biyu da rabi, rikicin da kuma ya raba kimanin mutane miliyan biyu da dubu dari da muhallansu