Amurka da Turai suna tattaunawa da gwamnatin kasar Yaman.

'Yan kasar Yaman na murna, shugaban kasar su Ali Abdullah Saleh ya tafi kasar Saudiyya.

Jami'an gwamnatin kasar Yaman da na bangaren adawar kasar sun gana daban-daban da jakadun Amurka da na Turai

Jami'an gwamnatin kasar Yaman da na bangaren 'yan adawar kasar sun gana daban-daban da jakadun Amurka da na Turai a jiya lahadi a daidai lokacin da shugaba Ali Abdullah Saleh ke murmurewa bayan an yi nasarar aikin tiyatar cire mi shi buraguzan kwanson makamai daga kirjin shi.

Ranar Jumma'a Mr.Saleh ya ji ciwo cikin wani harin da aka kai har harabar Fadar shi ta shugaban kasa. Daga bisani aka dauke shi ta jirgin sama zuwa wani asibitin sojoji a birnin Riyadh tare da wasu manya-manyan jami'an gwamnatin shi. Ana kyautata cewa shugaban na kasar Yaman zai yi makonni biyu a kasar Saudiyya.

Kusoshin jam'iyya mai mulkin kasar sun nace lallai sai dai Mr.Saleh ya koma kasar Yaman amma masu lura da al'amuran yau da kullum sun ce babu tabbas ko masu masaukin shi na kasar Saudiyya za su bar shi ya koma gida a matsayin shi na shugaban kasa.Kafin Mr. Saleh ya bar kasar Yaman ya mika mulki ga mataimakin shugaba Abd al-Rabb Mansur Hadi.

A jiya lahadi Mr.Hadi ya gana da jakadan Amurka a kasar Gerald Feierstein domin su tattauna hanyoyin samun hadin kan kawancen 'yan adawar kasar ta Yaman. Haka kuma Mr.Hadi ya gana daban da kwamandojin sojojin kasar wadanda su ka hada da 'ya'yan Mr.Saleh.

Jaridar "Washington Post" ta buga labarin cewa jakadun Amurka da na Turai, a cikin su da Feierstein, sun bukaci 'yan adawar kasar Yaman da su dakata kar su kafa kwamitocin mulkin wucin gadi kafin Mr.Saleh ya bar mulki kamar yadda ya kamata. Jaridar ta ruwaito wata mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka ta na cewa gwamnatin Amurka na ci gaba da kokarin neman karbe mulki daga hannun Mr.Saleh wanda abokin ta ne a wani lokaci.

Da yammacin jiya lahadi, an ga alamun cewa tsagaita wutar da Saudiyya ta taimaka aka samar ta na aiki tsakanin sojojin gwamnatin kasar da magoya bayan Sheikh al-Ahmar, shugaban wata kabilar masu adawa, al'amarin da ya kawo kwanciyar hankali ga mazauna Sana'a babban birnin kasar, wadanda ke cikin damuwa saboda dimbin mutanen da aka kashe a birnin cikin fadan makonni biyu.

Mr.Hadi ya umarci sojojin shi su fice daga wuraren da ke hannun 'yan adawa a babban birnin kasar, a yayin da al-Ahmar shi ma ya fara kwashe mayakan shi daga cikin gine-ginen gwamnati sannan ya yi kira a kawo karshen fadan.

Daga samun labarin cewa Mr.Saleh wanda ruwan rikici ya ciwo ya bar kasar, an barke da shagulgulan nuna murna a jiya lahadi a kasar ta Yaman. A Sana'a babban birnin kasar, mutane sun buge da rawa da waka tare kuma da yanka shanu a wurin da masu zanga-zanga su ka sawa suna dandalin canji. Amma kuma ana ta bayyana damuwa game da ko da gaske iyakacin mulkin Mr.Saleh na shekaru talatin da ukku kenan.

Tafiyar da Mr.Saleh ya yi daga kasar ba ta sa an daina tashin hankali ba. A garin Taiz 'yan bindiga sun farma harabar Fadar shugaban kasar, sun kashe sojoji hudu.

An ci gaba da balahira a kasar Yaman har bayan tafiyar Mr.Saleh kasar Saudiyya inda ya ke jinya.

Daga lokacin da jama'a suka fara boren nuna kin jinin Mr.Saleh a cikin watan janairu ya zuwa yanzu an kashe mutane kusan dari hudu a kasar ta Yaman.