Amurka Da Taliban Na Kokarin Samar Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Kungiyar Taliban da Amurka sun ce zasu kaimi a kokarin su na kammala shirya daftari a zaman su na wannan lokaci a kan tattaunawar zaman lafiya a kasar Qatar idan sun cimma matsaya a kan sasantawa a siyasance wurin kawo karshn yakin Afghanistan.

Haifaffen ba-Amurken Afghanitan kuma dan diflomasiya, Zalmay Khalid shine ke jagorantar rukunin Amurkawa a wannan tattaunawa a zagaye na bakwai wanda aka kwashe kusan shekara guda tsakanin bangarorin biyu a kan wannan yakin shekaru 18.

Tattaunawar da ake yi da wakilan Amurka domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ya gudana tsawo sa’o’I 12 ba tare da samun wani tsaiko ba a ranar Asabar, inji Suhail Shaheen da ya yi magana da yawun rukunin masu tattaunawa na bangaren Taliban. Masu tattaunawar Amurka da na Taliban suna nan suna aiki gadan gadan a kan daftarin yarjejeniyar, Suhail yana fadawa Muryar Amurka a jiya Lahadi.