Kasar Amurka da Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da nufin bunkasa wasan kwallon kafar ‘yan matan NIjar bayan da aka gano cewa dalilai masu nasaba da al’adu na zama wani shamakin da ke hana wa ‘yan mata buga kwallo, sabanin yadda suka rungumi sauran fannoni na wasanin motsa jiki.
Shirin dake tamkar wata matsakaiciyar kakar wasanni ya kunshi gangamin wayar da kan iyaye mahimmancin kwallon kafar ‘yan mata hade da taron bayar da horo ga masu horar da ‘yan mata a fannin kwallo yayin da su ma ‘yan matan suka samu horo akan wasu dubarun buga kwallo daga wasu Amurkawa Joanna Lohman da Staci Wilson wadanda suka zo Nijar takanas domin wannan aiki. Ali Mamadou Bague shine mai horarda ‘yan wasan kugiyar kwallon mata MENA NIger.
Gomman ‘yan matan da aka gayyato daga yankuna daban-daban na wannan kasa akasari daliban makarantun secondary ne aka garwaya da ‘yan wasan kungiyoyin kwallon kafar ‘yan sanda da ta Garde Nationale, abinda ya ba da damar karkasa su a rukunoni domin kafsawa.
Ita kuwa wannan ‘yar wasa mai sunan A’isha ta bukaci hukumomi su dauki wannan shiri da mahimanci domin a cewarta ‘yan matan Nijar a shirye su ke su daga tutar wannan kasa a fannin kwallon kafa.
Komai na wannan kakar wasanni ya gudana akan idon jakadan Amurka a Yamai Amb. Eric P. Whitaker domin tabbatar wa kansa cewa an yi abubuwa cikin nutsuwa kamar yadda aka tsara.
Ga wakilinmu a Yamai Sule Baram da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5