Amurka da Majalisar Dinkin Duniya Sun Yi Kashedin Barkewar Fada A Sudan ta Kudu

Riek Machar madugun 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu

A taruka biyu da aka yi a wurare daban daban jiya Laraba Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun fada cewa zaman tankiyan da ya tsanata yanzu alama ce ta yiwuwar barkewar wani sabon fada a Sudan ta Kudu

Wakilan Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedi a wurare taro biyu dabam dabam jiya Laraba a kan fargaba zaman tankiya da yiwuwar barkewartshin hankali a kasar Sudan ta Kudu.

Nan da nan wakilin Sudan ta Kudu a wurin wannan zama yamusunta wannan maganar kuma jakadan Sudan ta Kudu Kuol Alor Kuol Arop shima ya musunta cewar babu wani yunkuri shirya dakaru ko niyar kai wani mummunan farmaki da kasarsa ke yi a hirarsa da kamfanin dilancin labarun Associated Press.

A jiya Laraba a Juba babban birnin kasar, wasu masu kare hakkokin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedi a kan yiwuwar barkewar mummunar tarzoma ta kabilanci a kasar da yaki ya daidaita.