Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton Hillary Clinton ta bayyana cewa, Amurka zata kara maida hankali a yaki da cutar kanjamau, ta kuma ce tana kokarin ganin an shawo kan cutar baki daya.
Sakatariya Clinton ta bayyana haka ne a wajen taron kasa da kasa na yaki da cutar kanjamau da ake gudanarwa a Washington DC
Mrs Clinton tace Amurka ba zata yi kasa a guiwa ba kuma zata kashe kudin da ake bukata domin cimma wannnan burin. Ta kuma yi watsi da kushewar da ake yi cewa, Amurka bata kula da ganin bayan cutar da aka shafe shekaru 30 ana fama da ita ba.
Ta kuma bayyana cewa, tilas ne gwamnatoci su shawo kan yada cutar, yayinda tayi kira ga maza su amince a yi masu kaciya, yayinda tayi kira ga matan dake dauke da cutar kanjamau su kiyaye shawarwarin likitoci domin ceton rayukan jariransu.
Bisa ga cewarta, “wannan yaki ne da zamu iya nasara. Mun riga mun yi nisa, ba kuma zamu koma da baya ba.”