Amurka Da Italia Zasu Tattauna Akan Kasar Venezuela

  • Ladan Ayawa

Mideast Iran Venezuela Russia GECF Summit

Amurka da kaar Italia sun samar da wani taro domin duba matsalolin kasar Venezuela tare da ganin an samar da zaman lafiya da taimakon wadanda rudaninkasar ya rutsa dasu.

MDD tace Amurka da Italiya sun shirya su gudanar da wata taron tsaro na jeka nayi naka na MDD aka kasar Venuezuela.

Jakadiyr kasar Amurka a MDD Nikki Haley ita ce zata jagoranci wannan taron wanda za a gudanar a ranar littini, kuma taron zai hada da jawabi ne daga shugaban kula da jkare hakkin bil adama na MDD wato Chief Zeid Ra’ad Al-Hussain da kuma sakataren kungiyar jihohin Amurka Luis Almagro.

A cikin wata sanarwan da aka rarraba wa mahalarta taron an bayyana cewa taron zai bada damar duba yadda kasashen duniya da kungiyoyin kasa-da-kasa zasu taka rawar samar da zaman lafiya ta fannin siyasa tare da ganin an samu damar kai ayykan jin kai ga wadanda wannan zaman tankiyar ya rutsa dasu.

Wannan taron yana zuwa dai dai lokainda kasar ta Venezuela ke fuskantar yiyuwar gaza biyan bashi da ake binta.