Sakataren tsaron Amurka Ash Carter ya gaya ma manema labarai jiya Litini a hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon cewa Ministan Tsaron Indiya Manohar Parrikar ya rattaba hannu kan yarjajjeniyar a hukumance tunda farko a jiya. Dama Jjagororin tsaron biyu sun jimma amincewa kan yarjajjeniyar a bisa manufa, tun lokacin da su ka hadu a Indiya a watan Afirilu.
Carter ya ce an cimma yarjajjeniyar ce da amincewar bai daya, kuma za ta saukaka harkokin yau da kullum tare da ingantawa.
Jagororin tsaron biyu sun jaddada cewa yarjajjeniyar ba ta amince wata daga cikin kasashen ta kafa sansani a cikin dayar ba, amm kawai don amfani da sansanonin da kayan aikin tare idan bukatar hakan ta taso.
Yayin ziyarar da Parrikar ya kai Pentagon, jagororin tsaron biyu sun tattauna kan ayyana Indiya da Amurka ta yi kwanan nan a matsayin abokiyar tafiya kan batun tsaro.
An bayyana wannan ayyanawarce lokacin da Firaminista Narendra Modi ya ziyarci Washington DC a watan Yuni, kuma Carter ya ce yarjejjeniyar ta amince ma sojojin Amurka su hada kai da na Indiya ta hanyar da ba a yi sai da dadaddun kawayen Amurka na kud-da-kud.