Amurka Da China Sun Takawa Koriya Ta Arewa Birki Kan Gwajin Makami

Koriya ta arewa gwajin makami ya faskara biyo bayan barazanar da Amurka tayi na cewa zata yi amfani da karfin soja

Kasar Koriya ta Arewa bata samu damar kaddamar da gwajin makamin kare dangi ba a yau Asabar, bayan Amurka ta yi barazanar yin amfani da karfin soja a yankin haka kuma kasar China wacce take babbar kawa da kasar ta Koriya ta Arewa ta dogara da ita ta bangaren tattalin arzikin kasa ta kara kakabawa Koriya ta Arewa dokoki.

A maimakon haka Shugaban kasar ta Koriya ta Arewa Kim Jong Un yayi kallon faretin sojojin a biki ranar zagayowar wanda ya kafa kasar marigayi Kim Il Sung a ranar 15 ga watan Afrilu, ranar da ta kasance wata rana mai girma a kasar da ake wa lakabi da “Day Of The Sun” a turance.

Wani Mai fashin baki kuma wanda ya tsere daga Koriya ta Arewa Ahn Chan-il wanda ke aiki da Jami’ar Duniya ta Nazarin Koriya ta Arewa yace “ Kim Jon Un ya shirya yin yaki da Amurka, amma yayi watsi da shirin.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana cewar almu sun nuna ganin yadda ake tafiyar da aiyuka a Punggye-ri wajen da ake gwajin makamin kare dangi da kuma Pyongyang zsuyi gwajin wanda zai zo daidai da ranar haihuwar wanda ya kafa kasar. Tun a watan Janairun shekarar 2016 Pyongyang tayi ta kazar kazar ba tare da linzami ba, inda tayi gajin makami mai linzami mai matsakaici da kuma dogon zango . Haka kuma a wannan shekarar Kim Jong Un ya nuna cewar kasar na kan hanyar gama makamin mai Linzami mai nisan zangon Nahiya zuwa Nahiya wanda zai iya kai hari kan Amurka.