Amurka Da Bangladesh Zasu Kara Daukar Matakan Tsaron Kasashensu

Sakataren harkokin wajen Amurka da Faraministan Bangladesh

Firaministar Bangladesh Sheikh Hasina ta bayyana niyyar ta a fili ta hada kai da Amurka sosai game da yaki da ta'addanci, a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry, wanda ya bayyana cewa kasashen biyu sun amince su dau karin mataki na ganin jami'an leken asiri na tabbatar da tsaron kasashen biyu da kuma sojojinsu sun yi aiki tare don cimma wannan manufar.

Da ya ke amsa tambaya daga Muryar Amurka bayan wani jawabinsa a Dhaka, Kerry ya ce akwai alamar cewa kungiyar ISIS da ke Iraq da Siriya na da alaka da wasu kungiyoyi wajen 8 a fadin duniya, kuma daya daga cikinsu na Kudancin Asiya ne.

Kery ya kara da cewa masu tsattsauran ra'ayi a Iraqi da Siriya na tuntubar juna da wasu kungiyoyi a Bangladesh kuma wannan ba ko shakka daga jami'an gwamnatin da ya gana da su ciki har da Firaminista.

Kwararru kan harkokin ta'addanci a yankin sun zargi gwamnatin Hasina da jan kafa game da wannan alakar, a maimakon haka sai ta ke ta cewa wasu 'yan kasar ne ke kai hare-haren.