Duk da irin kokarin da shugaba Obama yayi na ganin ya shawo kan yan majilisar dokokin Amurka musammam masu shakku game da yarjejeniyar da aka cimmawa akan makamin Nuclear da kasar Iran hakan yayi karo da matsala.
Domin ko daya daga cikin manya-manyan masu dasawa da shugaban wato sanata Chuck Schumer ya fito sarari ya soki wannan batu.
An jiwo sanatanyana cewa biyo bayan nazari da tunane mai zurfi, na yanke hukuncin na soki lamirin wannan kudiri ta hanyar jefa kuriaar kin amincewa da wannan batu.
Shi dai Sanata Schumer, wanda yake wakiltar wata mazaba daga jihar New York yana daya daga cikin manya-manyan sanatoci Yahudawa, kuma ya bada sanarwar wannan matakin nasa ne jim kadan bayan dan majilisar wakilai dake sahun gaba a jamiyyar Democrat wanda shima Bayahude ne wato Eliot Engel daga jihar ta New York ya fitar da sanarwar nuna kyamarsa ga wannan shirin.
Sai dai sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry wanda shine jagoran wannan yarjejeniya yace sa kafa a yi fatali da wannan shirin ba shine abinyi ba domin saboda gaba.
Kerry na magana ne a taron manema labarai a ran gadin da yake yi a kasashen kudu maso gabashin Asiya