Amurka Babbar Abokiyar Kawancen Yankin Menkong Ce

Fadar White House

Kogin Mekong ya haɗa kusancin mutane miliyan 70 da kudu maso gabashin Asiya waɗanda ke dogaro da kogin don rayuwarsu, sufuri, da buƙatun makamashi. Amma saboda matsaloli a kowane lokaci suna iya tasowa su shafi miliyoyin mutane da ke wurin, kusan shekaru talatin da suka gabata Cambodia, Laos, Thailand, da Vietnam suka kafa Hukumar Kogin Mekong, ko MRC, ƙungiyar gwamnatoci don tattaunawar yanki da haɗin gwiwa kan sarrafa albarkatun ruwa da ci gaba mai ɗorewa.

Amurka a hukumance tana goyon bayan MRC a matsayin abokiyar haɓaka yankin.

A cikin watan Yuli na 2009, Amurka, Cambodia, Laos, Burma, Thailand, da Vietnam suka kafa shirin bunkasa yankin da suke kira da turanci “Lower Mekong Initiative” don haɓaka ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa a yankin. A cikin 2020, aka faɗaɗa shirin ya zama shirin hadin guiwa tsakanin Amurka da Mekong, shitin haɗin gwiwa, tsakanin ƙasashe biyar na abokan hulɗar yanki, tare da tallafi daga Amurka.

Don haka, Amurka ta maida kanta a matsayin abokiyar haɗin gwiwa wajen magance ƙalubalen iyakokin da yankin Mekong ke fuskanta. "Tare da abokan aikin mu na Mekong, muna karfafa kyakkyawan shugabanci, 'yancin tattalin arziki, da ci gaba mai dorewa ta hanyar inganta manufofi na gaskiya," in ji Sakataren Gwamnatin Amurka Antony Blinken a cikin rubutacciyar sanarwa.

Lallai, hadin guiwar wani ɓangare ne na babban tallafin da Amurka ta ke badawa a yankin don bunkasa shirin kungiyar ASEAN. A cikin shekaru da dama, shirin ya inganta rayuwar dubbun dubatan mutane a yankin Mekong. Duk da haka, ana samun sabbin ƙalubalen da suka zama mafi rikitarwa da su ka shafi wadansu kasashe, kamar rikicin canjin yanayi da cutar ta COVID-19.

"Don yaƙar barazanar da ta mamaye shekaru biyu da suka gabata-COVID-19-Amurka ta ba da alluran rigakafin miliyan 8.5 da kusan dala miliyan 60 na taimako I zuwa yanzu, ga ƙasashe a yankin Mekong, kuma za mu ci gaba da yin aiki tare da hukumomin lafiya na gida domin damarar yakar cutar da kuma.

Muna ba da waɗannan allurar rigakafin kyauta ba tare da sa batun siyasa ko tattalin arziki ba, ”in ji Sakataren Blinken a ranar 3 ga Agusta a taron ministoci na hadin gwiwar Mekong-Amurka.

Yace, "A wannan shekara mai zuwa, za mu iya sa ido tare don faɗaɗa haɗin gwiwa kan batutuwan da suka shafi yankin Mekong ba kawai ba, har ma da duniya baki ɗaya, gami da tallafawa, karfafawa mata, ƙarfafa tsarin kiwon lafiya don shirin cutar nan gaba, da haɓaka burin mu na yanayi."

Shirin hadin gwiwar "Mekong-Amurka yana aiwatar da matsayin Shugaba Biden cewa za mu iya shawo kan ƙalubalen duniya na yau ne kawai ta hanyar aiki tare. Yayin da muke yakar cutar da sake farfado da tattalin arzikin mu, kasashen yankin Mekong za su iya dogaro da Amurka abokan Mekong. ”