Kocin kungiyar kwallon kafar kasar Tanzaniya Emmanuel Amunuke, wanda kuma tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles dake tarayyan Najeriya ne, ya samu nasarar jagorantar tawagar kasar Tanzaniya ga samun tikitin halartar gasar cin kofin nahiyar kasashen Afrika, karo na farko cikin shekaru 39 da suka wuce.
Tanzaniya ta samu damar hakanne bayan da talallasa kasar Uganda da kwallaye 3-0 yayin wasan da suka buga a filin wasa da ke birnin Dar es Salaam, a ranar Lahadi 24 ga watan Maris 2019.
Rabon da Tanzaniya ta samun shiga cikin gasar ta nahiyar Afrika
tun a shekarar 1980 shekaru 39 kenan.
Tanzaniya ta kammala wasan neman tikitin gasar ne a matsayin jagorar, a rukunin da ita kuwa Uganda tana biye da ita, hakan ya basu damar halartar gasar cin kofin nahiyar ta Afrika (AFCON) wanda zai gudana a kasar Masar cikin shekarar 2019.