Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu dasake saduwa a wannan shirin na amsoshintambayoyinku.
TAMBAYA
"Assalama alaikum VOA HAUSA. Muna so ku tambaya mana masanan harkokin kasa-da kasa, kan yanda kasar Mali da Burkina Faso ke shirin kulla yarjejeniya da kasar RASHA, maimakon kasar Faranasa. Yaya lamarin zai kasance? Za a dinga koyar da harshen RASHAnci ne a makarantun Bokon kasashen, ko za a cigaba da amfani da harshen Faransanci ne. Kasashen biyu za su dinga amfani da takardar kudin CFA, wadda kasar Faransa ke buga musu ne Ko kuwa?"
Masu Tambaya: Babandi Mamman Bande, da Tasiu Unguwar Tudu, Damagaram da issuhu Madatai, da Ali Sarkin yakin Ni'ma, da shugaba Iliya Maishayi Garkin Daura.
AMSA: To idan masu tambayar, da ma sauran masu sha’awar jin amsar na tare da mu, ga amsar da wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo daga wurin PROF. Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano, kamar yadda za a ji a sauti.
Sai a kasance da mu makon gobe don jin kashi na biyu na amsar wannan tambayar da ma amsoshin wasu tambayoyin.
A yi saurare lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5