To tun bayan da aka shiga fama a Najeriya, sanadiyyar wasu dalilai, da su ka hada da matakan gyara da gwamnatin Najeriyar ta dauka, wasu da su ka tuna da hasashen da marigayi Shiekh Albani Zaria ya yi, kan yadda duk wata gyarar Najeriya za ta zo da wasu wahalhalun da ya zayyana dalla-dalla, su ka sake sakin wadannan faya fayen wa’azin nasa, ganin yadda bayanansa su ka zo daidai na abin da ke faruwa.
A daidai wannan lokacin masu sauraronmu da dama, sun shiga tambayar tarihin marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria, wanda mahaifansa ‘yan asalin Kano ne, amma aka haife shi a unguwar Muchia, Zaria, wasu ‘yan bindiga kuma su ka kashe shi ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2014.
To dayake a lokacin da ‘yan bindigar su ka yi wannan danyen aikin, an yi irin wannan tambayar akai akai, ta bukatar tarihin Sheikh Albani, kuma wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isah Lawan Ikara, ya samo amsa daga daya daga cikin daliban marigayin Daraktan makarantar Salafiyya ta Sheikh Albani da ke Zariya, Dr. Adulrafiyu Abdulganiyu, mun sake gabatar ma masu tambayoyi a yanzu waccen amsar.
Ga cikakken shirin ta sauti:
Your browser doesn’t support HTML5