AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Tarihin Abzinawa (Auzunawa) na Janhuriyar Nijar (1).

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Su na da alaka da wata kasar kuma? Su na da alaka da wata kabilar kuma?

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na AmsoshinTambayoyinku.

Yau za a ji kashi na daya na amsoshin tambayoyin masu sauraronmu da dama, da su ka hada da Adamu Aliyu Ngulde, da Buhari Yahaya Nguru, da Adamu Habu Umar Taura, jihar jigawa masu son jin tarihin Abzinawa (ko Auzunawa) na Janhuriyar Nijar, musamman ma ko shi sun a da alaka da wata kabila ko kuma wata kasa ta dabam.

To idan masu tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a Nyamai Sule Barma ya samo daga masanin tarihi, Farfesa Djibo Hammani na Jami’ar Abdou Moumouni Dioffo da ke Yamai.

A sha bayani lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

01-27-24 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU _ Tarihin Auzunawa.m4a