AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Takaitaccen Tarihin Marigayiya Sarauniya Elizabeth II

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Yau za a ji amsoshin tambayoyi kan wata mai dinbin tasiri a duniya, wato marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth II, wadda ta ga zamanai da dama ta kuma yi hulda da masarautu da hukumomi da Shugabannin kasashe da dama.

Masu sauraronmu assalama alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.

Yau za a ji amsar wata tambaya mai cewa:

Assalamu Alaikum VOA Hausa. Don Allah ku bamu tarihin marigayiya Sarauniyar Ingila, Elizebeth II. kuma shin da gaske ne, ita kadai ce ta ke da ikon tafiye-tafiye a tsakanin kasashen duniya, ba tare da fasfo ba? kuma an taba samun namiji da ya yi mulki a masarautar? ko yarima Charles ne na farko?.

Mai Tambaya: AMINU ADAMU MALAM MADORI A JAHAR JIGAWA, Najeriya.

Za kuma a ji maimaicin amsar tambayar hadin gwiwar nan ta su Malam Ango Malamin Makaranta Da Maimuna Sahabi Yawuri, masu cewa:

Assalamu Alaikum. Gaisuwa ga dukkan Ma'aikatan VOA HAUSA. Don Allah ku bamu cikakken tarihin sabon shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud. Wassalam.

Amsoshin:

To bari mu fara da amsar tambaya kan takaitaccen tarihin marigayiya Sarauniyar Ingila, Elizabeth, wanda malam Aminu Adamu da wasu masu saurarenmu ke son ji. Idan mai tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a Adamu, Muhammad Salisu Lado, ya samo daga malamin tarihi a kwalejin malamai ta tarayya (FCE) da ke Yola, jihar Adamawa, Najeriya, Dr Adamu Babikwai.

To sai kuma maimaicin amsar tambaya kan tarihin Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, wanda malam Ango Malamin Makaranta ya yi. Idan an tuna, wanda ya bayar amsar shi ne Dr. Idi Audu Girei, shi ma malami a kwalejin malamai ta tarayya da ke Yola, Adamawa, Najeriya.

A yi saurare lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

09-17-22 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3