AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: *Shin Yaya Turawa Su Ka Shigo Najeriya Har Su Ka Mulke Ta? * Yaya Tarihin Hausawan Sudan Ya Ke?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Kamar yadda mu ka saba, yau ma mu na dauke da amsoshin tambayoyi masu masu kayatarwa: Yadda Turawan mulkin mallaka su ka shigo Najeriya da kuma bambancin Hausawan Sudan da na Najeriya.

Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shiri na Amsoshin Tambayoyinku.

1. Tambaya: “Assalmu alaikum VOA Hausa. Shin ko ta yaya Turawa su ka shigo Najeriya har su ka mulke ta?"

Mai Tambaya: Sani Mailangelange Yawuri.

2. Tambaya: “Salam Muryar Amurka. Don Allah Ina son ku ba mu tarihin Hausawan kasar Sudan. Shin akwai wani bambanci tsakanin Hausawan kasar Sudan da na Najeriya?"

Mai Tambaya: Babangida IBB Giyawa Daga Karamar hukumar mulki ta gwaranyo jahar sokoto

Amsoshin

To bari mu fara da amsar tambaya kan yadda Turawa su ka shigo Najeriya har su ka mulke ta. Idan mai tambayar, Malama Sani Mailangelange da ma sauran masu saurare na tare da mu, ga amsar wannan tambayar da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Lado, ya samo daga Dr Babikwai Girei na Kwalejin Horas Da Malamai ta Tarayya (FCE) da ke Yola, Adamawa, kamar yadda za a ji ta sauti.

Amsa 2

Sai kuma amsar tambaya kan bambancin Hausawan Sudan da na Najeriya. Idan mai tambayar, Babangida IBB Giyawa, da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Lado, ya samo daga Malam Ibrahim Musa Audu na Kwalejin Horas Da Malamai ta Tarayya (FCE) da ke Yola, Adamawa, kamar yadda shi ma za a ji ta sautin.

A yi sauraren tambayoyin lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

10-01-22 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3