Yau za a ji maimaicin amsar tambayoyin da ke cewa: “Sashin Hausa Na Muryar Amurka (Voa), a yau ina so ku min karin bayani akan makamin nukiliya ko makamin kare dangi. Shin mene ne ma makamin nukiliya? Kasashe nawane a duniya su ke da wannan makamin? Ko akwai iya adadinsa da ake da shi yanzu a duniya? Ƙasashen da basu da irin wannan makamin ba zai yiwu su mallake shi ba ne? Ko an taba harba wannan makamin a duniya?”
To idan Mallam Sa’idu Abdullahi Damaturu da sauran masu saurarenmu na tare da mu, ga maimaicin amsar da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Mohammed Salisu Lado ya samo daga Dakta Mahdi Abba na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawa, Najeriya, wanda ya yi bayani kamar yadda za a ji a sautin:
Your browser doesn’t support HTML5