AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: *Mene Ne Tasirin Dalar Amurka A Hada Hadar Duniya? *Marayu Da Aka Rike Na Iya Cin Gado (ii)?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Wannan makon mun kammala gabatar ma ku da amsoshi kan batun gado da magada. Sannan kuma mu ka hada da amsar tambaya kan tasirin dala a hada hadar kudi na cinakayya ta kasashen duniya, inda kusan dalar ta zama ma'aunin darajar kowace takardar kudi.

Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu dasake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.

Tambaya 1

Yau za a ji kashi na biyu, kuma na karshe na amsar tambayar nan mai cewa: wadanda Allah bai ba su haihuwa ba, kuma suka dauki marayu shin marayun za su iya cin gadonsu?

Idan an tuna, masu tambayar su ne: Ayuba Isah da Malami Kurra daga garin Sarkin Noma, jihar Yoben Najeriya”

Tambaya 2:

Assalama alaikum VOA Hausa:

  1. Ko me ya sa dalar Amurka ke hawa da sauka?
  2. Shin tashin dalar Amurka na shafar tattalin arzikin duniya?
  3. Me ya sa kowace kasa a duniya ke amfani da dalar Amurka wajen musayar kudi da hadahadarsu?

Mai Tambaya: Alhaji Mainasara Nasarawa Funtua.

AMSA

To bari mu fara da kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambaya kan gado. Idan masu tambayar, da ma sauran masu saurare, na tare da mu, ga ragowar amsar da mu ka samo ma ku daga Wakilin Malaman Bauchi, Shugaban Majalisar Malaman Izala reshen Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, kuma Sarkin Malaman Duguri, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, wanda zai cigaba da bayani, kamar yadda za a ji idan an dangwali abin sauti.

Sai kuma tambaya ta biyu, wato tambaya kan tasirin dalar Amurka a hada-hadar duniya. Idan mai tambaya, Mainasara Nasarawa Funtua da ma sauran masu saurare na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a birnin Accra Hamza Adam, ya samo daga wani masanin tattalin arziki, kuma malami a Jami’ar Christ The King da ke Ghana, Dakta Najeeb Ibn Hassan, wanda shi ma za a ji idan an dangwali abin sauti.

Sai a dangwali abin sauti a ji cikakken shirin :