Kamar yadda mu ka ce a makon jiya, bambancin tsarin Shugaban Kasa da Firaminista abu ne da ya shige ma mutane da dama duhu. Don haka amsar wannan tambayar za ta amfani masu sauraronmu da dama, musamman ma wannan babi na karshe.
Washington, D.C. —
Masu sauraronmu assalamu a laikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku:
Tamabaya
Assalamu alaikum VOA Hausa. Don Allah ku ba ni haske dangane da tsarin mulkin Shugaban kasa da na Firaminista. Wanne ne daga cikin su biyun zai fi amfanar talaka?
Mai Tambaya: Malam Malami Kura Garin Sarkin Noma Jahar Yobe, Najeriya.
Amsa
Idan mai tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga kashi na biyu kuma na karshe na amsar da wakilin Muryar Amurka a shiyyar Adamawa da Taraba, Muhammad Salisu Lado, ya samo daga Dakta Mahadi Abba, malami a Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola Jahar Adamawa Najeriya.
A sha bayani lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5