AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Me Ya Sa Kasashe Kan So Mallakar Makamin Nukiliya?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Yau mun zo ma ku da amsoshin tambaya kan hikimar mallakar makamin nukiliya. Ma'ana: me ya sa kasashe kan bukaci mallakar wannan mugun makamin?

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.

TAMBAYA:

“Don Allah a tambaya ma na masana siyasar duniya. Ko mece ce hikimar kasa wajen mallakar makamin nukiliya? Ko me yasa manyan kasashe ke hana Iran da Koriya ta Arewa mallakar nukiliyar?”

MASU TAMBAYA: Zakaria Salifu Gidan Rumji da Adamu Shamuwa mai Dawaki Shikal Jamhuriyar Nijar.

AMSA: To idan masu tambayar na saurare, ga amsar da wakilinmu a Shiyyar Adamawa, Najeriya, Muhammad Salisu Lado, ya samo maku daga Dr Adamu Babikwai, malami a Kwalejin Malamai ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke Yola, jihar Adamawa, wato F C E Yola.

A sha bayani lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

02-11-23 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU - ok.mp3