AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: *A Ba Mu Tarihin Bawa Jangwarzo *Ta Yaya Gidajen Jaridu Ke Samun Kudaden Tafi Da Harkokinsu?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Kamar yadda aka saba, wannan karon ma mun samo maku amsoshin wasu tambayoyi masu muhimmanci --- kan takaitaccen tarihin Malam (Sarki) Bawa Jangwarzo; da kuma yadda gidajen jaridu ke samun kudaden gudanar da harkokinsu.

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shiri na Amsoshin Tambayoyinku.

Tambaya 1

Assalamu Alaikum VOA Hausa. Don Allah ku ba mu tarihin mashahurin malamin nan Bawa Jangwarzo,

Masu Tambaya: Aminu Adamu Malam Madori, da Malam Musa Danmalam Mai Wankin Hula Garbo Miga, jahar Jigawa, Najeriya.

Tambaya 2:

Salam VOA Hausa. Don Allah ina so ku tambaya min masana. Shin ta wace hanya gidajen radiyo ke samun kudi domin biyan ma’aikatansu albashi? Shin cikin ma’aikatan akwai wadanda suka fi wasu albashi?

Mai Tambaya: Babangida IBB Giyawa daga Karamar Hukumar mulki ta Gwaranyo jahar Sokoto.

AMSA

Ta farko:- To bari mu fara da amsar tambaya kan tarihin Bawa Jan Gwarzo. Idan mai tambayar, da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a Shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Garba, ya samo daga Malan Idi Audu Girei, malamin tarihi a Kwalejin Horas da Malamai ta Gwamnatin jihar Adamawa, da ke Hong, wanda ya yi bayani kamar yadda za a ji idan an dangwali abin sauti.

Ta biyu:- Sai kuma amsar tambaya kan yadda gidajen jaridu ke samun kudaden tafi da harkokinsu. Idan masu tambar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, har ila yau ga amsar da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Garba, ya samo daga Dr. Adamu Babikwai, malami a Kwalejin Horas da Malamai ta Gwamnatin Tarayya da ke Yola, Adamawa, Najeriya, wanda shi ma ya yi bayani, kamar yadda za a ji idan an dangwali abin sauti.

To sai a kasance da mu makon gobe don jin amsasohin wasu tambayoyin, idan Allah ya kaimu.

A yi saurare lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

12-17-22 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3