Amnesty Ta Zargi Sojojin Myanmar Da Laifukan Yaki

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi sojojin Myanmar da aikata laifukan yaki da ta’asa da cin zarafi a jihar Rakhine da ke arewa maso yammacin kasar, inda rundunar sojan ta fattataki al'ummar musulmin Rohingya kasa da shekaru biyu da suka wuce.

Sojojin sun tura dubban dakaru zuwa Rakhine don yaki da kungiyar 'yan tawaye ta Arakan, wadanda ke neman karin 'yanci daga 'yan mabiya addinin Buddha na jihar.

A cikin wani rahoto da aka wallafa a yau Laraba, kungiyar kare hakkin bil adama din ta jera abin da ta kira "manyan laifukan yaki" masu yawa da sojojin Myanmar suka aikata, ciki har da kisan gilla, da kama mutane ba bisa ka’ida ba, da azabtarwa da kuma batar da su.

Darektan yanki na kungiyar ta Amnesty na shiyyar gabas da kudu maso gabashin Asiya, wato Nicholas Bequelin, ya ce ayyukan da sojoji suka yi a jihar Rakhine "sun nuna rashin imani da adalci daga sojojin ga fararen hula."