Amnesty International Ta Tattaba Bayanan Cin Zarafin Musulmin Rohingya a Myanmar

Musulmin Rohingya dake gudun hijira bayan an kone gidajensu

Kungiyar kare hakkin bil Adama ko Amnesty International ta ce ta tara bayanai da shedu da zasu tabbatar jami'an gwamnatin Myanmar da suka hada da wani babban janar na soji sun ci zarafin musulmin Rohingya

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta Amnesty tace ta tattara muhimman shedu dake tabbatarda jami’an Myanmar 13, ciki har da wani babban kwamnadan sojoji sun aikata lafin cin zarafin bil adama a loakcin da suke kai hari a kan Musulmin Rohingya a cikin watan Agusta


An gano babban kwamandan ma’aikatar tsaron kasar, Janar Min Aung Hlaing da wasu manyan jami’an soja guda takwas da ma wani kurtun soja da wasu yan sandan tsaron kan iyaka guda uku a cikin rahoton kungiyar Amnesty mai shafi 200.


Kada ma ayi kuskure ace babu wani laifin take hakkin bil adama da aka aikata, saboda muna batun laifuka ne kamar fyade, da kisa da azabtarwa da hana abinci da binne nakiyoyi da kuma kona kauyuka da dama inji darektar kai agaji lokacin bala’i na Amnesty Tirana Hassan, yayin da take kaddamar da rahoton a shekaranjiya Litinin. Tace wadannan wasu manyan laifuka ne da zasu kai kara gaban kotun manyan laifuka ta kasa da kasa.