Amirka ta azawa shugaban kasar Venezuela takunkunmi

Shugaban kasar Venezuel Nicolas Maduro ke murnar zaben da aka yi a kasar sa

A saboda abinda ta kira haramtaccen zaben sabuwar Majalisar da aka yi a kasar Venezuela, Amirka ta azawa shugaban kasar takunkunmi

Amurka ta azawa shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro takunkunmi, saboda abinda ta kira “haramtaccen zaben sabuwar majalisar da aka yi, wanda zai ba da damar a sake rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar.

A halin da ake ciki, an hanawa shugaba Maduro amfani da kadarorin da ya mallaka a nan Amurka, sannan an haramtawa Amurkawa yin kowace irin huldar kasuwanci da shi.

A jiya Litinin Sakataren Baitul-malin Amurka, Steven Mnuchin ya bada sanarwar azawa shugaban wannan takunkumi a nan Washington, inda ya kira Shugaba Maduro a matsayin mai “mulkin kama karya” wanda yake watsi da ra’ayin ‘yan Venezuela.

A mako mai zuwa idan Allah ya kaimu kasar Peru ta za ta gudanar da wani taron ministocin harkokin kasashen waje na yankin Latin Amurka a Lima, domin tattauna rikicin na Venezuela