Shugaba Barack Obama yae Amirka da kasar Saudi Arabiya zasu ci gaba da yin aikin tare wajen dakile aiyukan ta'adanci a gabas ta tsakiya da duniya ga bakin dayanta ciki harda yaki da ake fafatawa da yan yakin sa kan kungiyar Islamic State.
Mr Obama yace Amirka da Saudi Araiya suna nuna damuwa akan yadda al'amurra suka kasance a kasar Yamal da kuma bukatar dake akwai na maida gwamnatin kasar bisa turba da kuma damuwar da Saudi Arabiya ke nunawa akan rikici kasar Syria.
Shugaba Obama yayi wannan furucin ne kafin ya gana da Sarki Sulaiman na Saudiya a fadar White House a jiya Juma'a. Wannan ce ziyarar farko da sarki Sulaiman ya kawo nan Amirka tun lokacin da aka nada shi bisa wannan mukami a watan Janairu bayan rasuwar sarki Abdullah.
Shugaban na Amirka yace da shi da sarki Sulaiman sun tattauna batun kaddamar da yarjejeniyar da giggan kasashen duniya suka kula a kwananan nan da nufin dakile shirin nukiliyan Iran.
Ita dai kasar Saudi Arabiya tana nuna dari dari akan yarjejeniyar kuma tana daukar Iran a zamar matsala a yankin.
Ganawar da shugabanin biyu suka yi jiya Jumaa, itace ganawar farko tun taron kolin da aka yi a ranar sha hudu ga watan Mayu, lokacinda shugaba Obama ya yiwa shugabanin kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf bayani akan yarjejeniyar da ake son kulawa da Iran akan shirin nukilyarta akan damuwa da kasashen yankin ke nunawa.