Amirka da kasar Taiwan suna matsawa China lambar ta sako bijirarrun da take tsare dasu

Masu zanga zangar rike da kandir a dandalin Tiananmen kasar China.

Amirka da kasar Taiwan suna matsawa kasar China lambar ta sako bijiraru kuma ta binciki mununar murkushe masu zanga zangar hankoron kafa mulkin democradiya a dandalin Tianamen shekaru ashirin da biyu da suka shige

Amirka da kasar Taiwan suna matsawa kasar China lambar ta sako bijiraru, kuma ta binciki mununar murkushe masu zanga zangar hankoron kafa mulkin democradiya a dandalin Tianamen shekaru ashirin da biyu da suka shige.

A jiya juma’a ma’aikatar harkokin wajen Amirka ta gabatar da sanarwa a jajibirin bikin mumunar murkushe masu zanga zangar da China tayi a ranar hudu ga watan yunin alif dari tara da tamanin da tara, lokacinda gwamnatin China ta tura tankoki dandalin Tinamanen domin su murkushe zanga zangar da dalibai da ma’aikata suka yi makoni suna yi.

Kila daruruwa ko kuma dubban mutane ne suka mutu a lokacin da aka yi wannan murkushewa. Ma’aikatar harkokin wajen Amirka ta bukaci China ta baiyana wadanda aka kashe ko aka kama ko kuma suka bace, kuma ta kawo karshen musgunawa wadanda suka halarci ganganmi da su da iyalansu.

Haka shima shugaba Taiwan Ma Yin Jeou yayi kira ga China data bi sahun kasarsa Taiwan ta kaddamar da sauye sauyen harkokin siyasa. A yau asabar dubban yan kasar China da yan wasu kasashe masu yawon bude ido ne suka taru a dandalin Tinamen inda aka dauki tsauraran matakan tsaro.