Aminu Muhammad Malami yace mana bayan kamala karatunsa na jami’a, abin da ya fara shine lura da irin abinci da ake ci, mussaman ma a yankin arewa. Kasancewar ya karanci harkan noma da muhalli, hakan ne ya sa yayi tunanin sarrafa masara zuwa gari.
A yanzu haka dai, matashin na da kimanin ma’aikata 80 da suke aiki a karkashinsa, inda suke sarrafa masara, alkama, dawa da kuma samar da man-gyada, kamar yadda matashin ke fadi kimanin shekaru 4 kenan da ya fara wannan sana’a.
Ya kara da cewa, ya samu wata kwangila da hukumar lura da abinci na duniya wanda zai samawa 'yan gudun hijira. Inda zai samar da kimanin mota 200 ga 'yan gudun hijira domin saukaka musu wajen sarrafa shi.
Daga cikin kalubalen da yakan fuskanta, yace da farko babban abin da ya ci masa tuwo a kwarya shin, rashin samun lambar NAFDAC. Inda ya shafe kimanin shekara daya da rabi kafin ya samu.
Daga karshe dai ya ce, babban burinsa dai bai wuce nan da 'yan shekaru ba ace ya dauki matasa akalla 500 aiki a kamfaninsa.
Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar mu da matashi mai kananan sana’oi, yadda ya fara da irin nasarori da kalubalen da ya samu kafin ya kai inda yake.
Your browser doesn’t support HTML5