Amfanin shayar da yaro da nonon uwa

Taron Fadakar Da Mata

Shayyar da yaro da nonon uwa yana da amfani wajen kare mace kasadar kamuwa da cututtuka, da kuma hana ta dade tana jinin biki

Dr. Rukayya Wammako kwarariyar likita ce mai kula da lafiya mata da yara a hukumar lafiya matakin farko. Tace akwai wani abinda mutane basu sani ba, ko kuma dai mata basu gane ba.

A lokacida mace take shayar da danta, akwai wani ciwo da mata suke ji cikin mahaifar su, sai suji ciwon ya tsanata a lokacinda yaro yake tsotson nono. Wannan yana daya daga cikin dalilin daya sa wasu mata basu son shayarwa.

Dr. Rukaiyya tace a gaskiya da mace zata daure wannan zafi ko ciwo, ta kuma san alfanun dake tattare cikin sa, to da mata sun ci gaba da shayar da yayan su komai zafi ko ciwo.

Domin tace a lokacinda yaro ke tsotson nono, akwai sako mai amfani da yake kaiwa kwakwalwa. Haka kuma daya daga cikin alfanun shayarwa shine mace ba zata dade tana jinin biki ba.

Wakilin sashen Hausa Nasiru El Hikaya ya zata da dr. Rukkaiya Wammako.

Your browser doesn’t support HTML5

Alfanun shayar da yaro da nonon uwa 2"12