Ambaliyar Ruwan Tsunami Ta yi Barna A Indonesia

Yau Litinin, Shugaban Indonesia Joko Widodo ya zagaya don gane ma kansa irin barnar da ambaliyar ruwan tsunami ta yi, a mashigar ruwan Sunda na kasar. Shugaban ya duba barnar da ta auku a otal din Mutiara da ke gandun shakatawar nan na gaban ruwan Carita da ke lardin Banten.

Hukumar kai daukin gaggawa ta Indonesiya ta bayyana yau Litini cewa jimlar mutanen da su ka mutu zuwa yau ya kai 281, kuma mutane 1,016 sun ji raunuka, sannan ana neman mutane 57.

Mai magana da yawun Hukumar kai Daukin Gaggawa ta kasar, Sutopo Purwo, ya ce adadin wadanda su ka mutu zai cigaba da karuwa.

Hukumar Nazarin yanayi da karkashin kasa (BMKG a takaice), ta ba da rahoton aukuwar aman wuta a Tuddan Krakatoa da misalin karfe 9 na dare agogon yankin, ranar Asabar, daga bisani kuma, bayan kimanin minti 30, sai ambaliyar ruwan tsunami ya auku.