Tun kafin daminar ta shekarar 2022 ta fadi masana sunyi hasashen samun ambaliya mai tsanani, wanda wannan ambaliya tayi barna tare da haddasa rasa rayuka da dukiyoyin al’umma, wanda ya haura irin wanda ya faru a shekaru goma da suka gabata wato na shekarar 2012.
Duk da cewa hukumomi sun alakanta wannan ambaliyar ruwa da canzin yanayi da kasashen duniya ke fuskanta, gwamnatin kasar ta nuna alhininta kan irin barnar da aka samu.
Ministar jinkai da kare faruwa iftilai ta Najeriya Sadiya Umar Farouk tace gwamnati ta tallafawa duk wadanda wannan bala’i ya shafa, a inda ta ce kasar tayi asarar dukiyoyin da kudinsu ya Kai sama da dala biliyan shida.
Wani wanda wannan ambaliyar ruwan ta bara ya shafa ya ce, tallafin da ake baiwa al’umma ba kasafai yake zuwa gun wadanda abun ya shafa ba, ya kara da kokawa kan yadda gwamnati ta kasa yin wani shiri don kare faruwar ambaliyar ruwan.
Kome gwamnatin Najeriya keyi kan hasashen kara samu mummunar ambaliyar ruwa a daminar bana?
Jihar Jigawa dai ita ce aka ayyana a matsayin jihar data fi kowacce samun wannan matsala ta ambaliyar ruwa a bara.
Saurari rahotan Alhassan Bala:
Your browser doesn’t support HTML5