Ambaliyar Ruwa Zata Haifar Da Matsalar Rashin Abinci

NIGERIA-FOOD/FLOODS

Alkalumman sun nuna cewa s mutane 170 ne suka mutu, sannan ambaliyar ta raba wasu dubu 2,005 da muhallansu a jihohi 28 cikin jihohi 36 na kasar.

Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta yi kashedi cewa asarar rayukan da aka samu sakamakon mummunan ambaliyar ruwa a kasar yana iya tsanani a watannin Satumba da Oktoba, lokacin da aka fi samun ruwan sama kamar da bakin kwarya. Tuni ambaliyar ta kashe sama da mutane 170, sannan ta raba dubban mutane da muhallan su a kasar cikin wannan shekarar.

Alkalumman da hukumar ta NEMA ta tattara karkashin tsarin da ta shimfida da zummar bibiyan lamarin, ya nuna cewa mutane 170 ne suka mutu, sannan ambaliyar ta raba wasu dubu 2,005 da muhallansu a jihohi 28 cikin jihohi 36 na kasar.

Ambaliyar ta fi kamari a jihohin Bauchi, Zamfara, Sokoto, Neja, da Jigawa.

Mai Magana da yawun hukumar ta NEMA Ezekiel Manzo ya zanta da Muryar Amurka cikin harshen turanci inda ya ce “A yanbzu muna kan aikin kai dauki a wurare da dama indaaka samu ambaliyar ruwan. Batun ambaliyar ruwan ba zai kare yanzu ba saboda yanzu ne damina ta yi nisa sosai. Lamarin da muke fuskanta yafi kamari a arewacin Najeriya, sannan ya ce rahotannin da muke samu, ana samun karuwan ruwa a kogin Benue da na Neja. Kuma idan ruwa ya ci gaba da karuwa a wadannan kogunan, zai batse ya yi ambaliya a cikin kasar mu, dan haka muna hasashen samun ruwa mai yawa daga jamhuriyar Nijer.”

Shi kuma Umar Namadi, gwamnan jihar Jigawa, daya daga cikin jihohin da ambaliyar tayi barna mai yawa, ya shedawa kafar yada labaran Al-Jazeera cewa bala’in ya karkatar da muhimman kudaden gwamnati.

Ya ce “An maida hankali sosai a kan wannan wajen saboda za'a bukaci ta magance wannan matsalar. A dalilin haka, tabbas harajin gwamnati da dama zasu salwanta. Baya ga haka kuma, gwamnati zata kashe Karin wasu kudade.”