Ambaliyar Ruwa Yayi Barna a Damagaran, Jamhuriyar Nijar

Ambaliyar ruwa a Damagaran, Nijar

Ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya a Damagaran ya haddasa rushewar gidaje da cikar salga sanadiyar cike magudanar ruwa da shara da ma gada lamarin da ya hana ruwan gudu.

Wasu mutane a wasu unguwanni a birnin Damagaran na kokawa da irin halin da suka shiga sanadiyar ambaliyar ruwa da ko ya kwashe gidajensu ko kuma ya cika masu gidaje biyo bayan wani ruwan sama da aka tafka..

Sun yi kira ga hukumomi su kwashe gada domin ruwan ya samu hanyar gudu saboda idan ba'a kwashe ba sauro zai damesu da yaransu.

Wata tace tsakiyar dakinsu ruwa ya cika makil.Katangar gidansu duk ta rushe saboda ruwan amma wai basu da halin gyarawa. Sun kai kukansu wurin mahukunta amma basu basu amsa ba.

To saidai Dr Bashir Sabo babban magajin garin Damagaran cewa yayi ba sun yi watsi da bukatun mutanen garin ba ne amma suna neman hanyoyin tasan ma lamarin duk da karancin kayan aikin da suke fama dashi. To saiadai yace ko an yi aikin za'a koma gidan jiya idan mutane basu daina zuba shara cikin gada ba. Da zara sun sami kayan aiki zasu sake hake magudanar ruwa tare da kiran jama'a da su daina zuba shara a wuraren da zasu hake. Haka ya kira jama'a da su daina zuba shara cikin gadoji.

Ambaliyar Ruwa

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ambaliyar Ruwa Yayi Barna a Damagaran, Jamhuriyar Nijar - 3' 41"