To saidai tun kafin wannan gargadin daga Mali wasu wuraren dake gabar teku a Nijar sun samu ambaliyar ruwa inda wasu gonakin shinkafa suka nitse yayinda ruwa ya mamayesu.
Wasu kungiyoyin dake zaman kansu da gwamnatin Nijar sun fara yunkurin karfafa wani babban shamaki tsakanin kogi da wasu unguwannin birnin Yamai kodayake tuni ruwan ya fara mamaye wasu wurare bayan ya nitsar da wasu gonakin shinkafa.
Ministan ayyukan jinkai na Nijar Lawal Magaji dake ziyartar yankin da abun ya shafa yace mutanen dake zaune a bakin ruwa ko wuraren da ruwa ke ci su hanzarta su kaura zuwa inda za'a kebe masu. Yace sun samu labarin ruwan ya fi karfin Mali kuma yana kwararowa zuwa Nijar. Bugu da kari ruwan sama ya kara dagula lamarin.
Sai dai abun ban tausayi shi ne manoma shinkafa da suka soma murmurewa daga barnar da ambaliyar ruwa ya haddasa masu a shekarar 2012 sai kuma gashi bana sun soma hasarar gonakinsu.
Ambaliyar ruwan zata shafi manoma da manyan 'yan kasuwa dake basu kudi su yi noma.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5