Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu unguwannin cikin Maiduguri da su ka hada da Londonciki, da Bolori da Gwange Police Barack da Blablingarnam da Jajeri da Maiduguri da Gwaidangari da dai sauransu, inda har mazauna wuraren su ka yi ta ficewa zuwa wasa wuraren, al’amarin da ya sa har sai da gwamnan jahar ya zagawa don gane ma idanunsa.
Wakilinmu a Maiduguri Haruna Dauda ya ji ta bakin wasu daga cikin ‘yan irin wadannan unguwannin, ciki har da wata mai suna Hajiya Amina, wadda ta ce gidansu ya lalace kwatakwata kuma a waje su ke sanadiyyar ambaliyar ruwan da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya. Ta yi kira ga gwamnati ta kai masu dauki saboda gidaje sama da ashirin ambaliyar ta lalata a unguwar kawai. Wani magidanci a unguwar Umarari ya ce sun shafe sama da shekaru biyar su na fama da ambaliyar ruwan – musamman ma a lokutan damina - ba tare da an taimaka masu ba. Ya ce hatta lamba tu da kansu su ke tonawa, don haka bai da girma kuma bai da zurfi. Don haka ya na kira ga gwamnati ta gina masu lamba tu mai kyau.
Haruna Dauda ya tuntubi shugaba hukumar tsabtace muhallin jahar Borno Alhaji Nasiru Ali Surundi wanda ya ce gwamnati ta kafa wani kwamiti don duba yanayin magudanan ruwa a wuraren. Y ace dama hakkin gwamnati ne ta samar da abubuwa irin haka. Don haka, in ji shi, idan kwamiti din ya kammala aikinsa aka kuma aiwatar da shawararsa, matsalar ambaliyar za ta zama tarihi.
Your browser doesn’t support HTML5